in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kashin karshe na 'yan tawayen Syria ya bar birinin Homs
2017-05-22 10:04:46 cri
An kwashe kashin karshe na 'yan tawayen Syria daga tungarsu dake Al Waer, al'amarin da ya ba gwamnatin kasar samun cikakken iko da birnin Homs.

Motocin safa na karshe dauke da 'yan tawayen da iyalansu sun bar Al Waer, wanda ya kasance tungar 'yan tawayen ta karshe a birnin Homs.

Kwashe 'yan tawayen ya biyo bayan wata yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin kasar a shekarar 2015, wadda ta ba su damar wucewa lami lafiya ta yankunan da suka mamaye dake arewacin kasar.

Aiwatar da yarjejeniyar ya gamu da matsaloli da dama kafin a sake farfado da shi a watan Maris da ya gabata.

A cewar gidan talabijin na kasar, tun daga watan Maris, kashin-kashin 'yan tawaye 12 da iyalansu ne suka bar Al-waer, abun da ya kawo adadin wadanda aka kwashe zuwa sama da 17,000, wadanda 7,000 daga ciki suka kasance 'yan tawaye.

Kididdiga a baya ta nuna cewa, yawan mazauna Al-Waer, da dakarun gwamnati suka yi wa kawanya tun a shekarar 2014, ya kai 300,000 kafin barkewar rikicin da aka shafe shekaru 6 ana yi a kasar, amma daga baya adadin ya ragu zuwa 75,000.

Sake samun iko da yankin babbar nasara ce ga gwamnatin Syria, al'amarin da zai ba ta damar samun cikakken iko da Homs, gari mafi girma na uku cikin biranen kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China