in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu ta yi watsi da hukuncin da kotun ICC ta yanke kan batun shugaban Sudan
2017-07-07 10:45:10 cri
A jiya Alhamis ne, majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu ta sa kafa ta shore hukuncin da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) ta yanke cewa, kasar ta gaza sauke nauyin dake kanta na kin kama shugaban Omar al-Bashir na Sudan a lokacin da ya halarci taron kolin AU da ya gudana a kasar a watan Yunin shekarar 2015.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da dangantaka da hadin gwiwar kasa da kasa Siphosezwe Masango ne ya bayyana hakan. Ya ce ya kamata ICC ta yi la'akari da cewa, taron kolin AU ne ya kawo shugaban na Sudan, ba gwamnatin Afirka ta kudu ce ta gayyace shi ba. Don haka yana da rigar kariya kamar sauran shugabannin kasashe. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China