Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, dole ne kasar Sin ta kyautata kwarewarta a fannin tsaron kanta, a kokarin kiyaye hakkokinta a sassa daban daban na duniya yadda ya kamata, tare da ba da gudummowa wajen kare zaman lafiya a duniya da ma shiyya-shiyya.
Ministan ya fadi haka ne a jiya yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru dangane da yadda jirgin ruwan yaki na farko da jiragen saman yaki ke sauka a kansa da kasar Sin ta kera da kanta ya shiga teku, a yayin taron manema labaru da ya yi da mataimakin shugabar kasar Jamus kuma ministan harkokin wajen kasar mista Sigmar Gabriel a birnin Berlin a wannan rana.
Wang Yi ya kuma jaddada cewa, akwai wani abu da kowa ya sani, kuma ba za a sauya shi ba, wato kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan tsaron kasa, a maimakon kai hari, kuma ba ta da aniyar mamaye wasu kasashe. Kasar Sin na kokarin raya huldar hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen duniya don samun nasara tare. Tana kuma sa ran bullo da makomar bai daya cikin hadin gwiwar kasa da kasa. (Tasallah Yuan)