A cewar Wu Qian, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar neman ci gaban kasa ta hanyar lumana, kana dukkan matakan tsaron da kasar ke dauka, domin kare kanta ne kawai.
Jami'in ya kara da cewa, a 'yan shekarun nan, sojojin kasar Sin sun halarci ayyukan kiyaye zaman lafiya, da ba da kariya ga jiragen ruwa, da ceton jama'ar da bala'i daga indallahi ya ritsa da su, abin da ya sa suka samu yabo daga gamayyar kasa da kasa. Saboda kasar Sin ba ta da niyyar kwace wasu yankuna, ko kuma neman zama kashin dankali a wasu wurare, don haka ta kasance kasar dake kokarin kiyaye zaman lafiya a duniya a ko da yaushe.
A karshe, jami'in ya ce, kasar Sin na fatan ganin kasar Amurka za ta iya kallon ci gaban aikin tsaron kasar Sin bisa wani ra'ayi mai adalci, da kokarin kyautata huldar dake tsakanin sojojin bangarorin 2.(Bello Wang)