Merkel ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, bayan an tabbatar da cewa Anis Amri, dan kasar Tunisiya wanda ake zargi da kaddamar da harin kasuwar sayar da kayayyakin kirsimeti a birnin Berlin, cewar an kashe shi, kuma jami'an yan sandan kasar Italiya ne suka harbe shi a lokacin wani sintiri a Milan da safiyar jiya Juma'a.
Harin na kasuwar kirsimetin ya haifar da tambayoyi iri iri, Angela Merkel ta bayyana cewa gwamnatinta a shirye take ta dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron kasar.