A ranar 18 ga wata ne dai shugaba Trump ya rubuta wani sako a dandalin sada zumunci, yana mai cewa, kasar Jamus ta ci bashi da yawa daga NATO, kuma Amurka na samar da tsaro mai nagarta da tsadar gaske ga kasar ta Jamus, don haka kamata ya yi Jamus ta saka mata.
Ministar ta ce, NATO ba ta ajiye kudin da za a ci bashi, kuma kasar Jamus ta yi alkawarin kara kasafin kudin tsaron ta da kashi 2 cikin dari bisa GDPn ta, amma ba daidai ba ne an hada wannan hasashe da kungiyar NATO. Ta ce, za a yi amfani ne da kasafin kudin tsaron na Jamus, wajen ayyukan kiyaye zaman lafiyar MDD, da na murkushe ta'addanci da dai sauransu. (Bilkisu)