in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa da kasar Jamus a cikin kungiyar G20
2017-04-27 09:50:07 cri
Ministan harkokin wajen Kasar Sin Wang Yi, ya ce a matsayinta na abokiyar hulda Jamus ta kowacce fuska, a shirye Kasar Sin take ta goyawa Jamus baya, domin ta karbi bakuncin taron kungiyar G20 masu karfin tattalin arziki a duniya, a birnin Hamburg na kasar, tare kuma da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen a cikin kungiyar G20.

Wang Yi, wanda ke Jamus domin halartar muhimmin taro tsakanin kasar Sin da Jamus kan harkokin diflomasiyya da tsaro, ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da mataimakin shugaban Gwamnatin Jamus kuma Ministan harkokin wajen kasar Sigmar Gabriel.

Ya ce taron G20 da zai gudana a Hamburg, zai dora ne a kan nasarorin da aka samu yayin taron da aka yi a bara a Hangzhou na Kasar Sin, tare da ci gaba da kokarin habaka tattalin arzikin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China