Kamfanin ya ruwaito wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar dake cewa, wani ayarin sojojiin kasar dake aiki a lardin Tipaza, ya kashe wani dan ta'adda a yankin Murad a jiya Lahadi, sai dai sanarwar ba ta ambaci sunan dan ta'addan ba.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, ayarin dake aikin sintiri ya kuma kwace bindigar ruwa da abubuwan fashewa a lardin Adrar dake da nisan kilomita 1600 daga kudancin Algiers.
Rundunar ta ce wannan aikin ya kuma tabbatar da yadda sojojin da sauran jami'an tsaro ke mai da hankali ga yaki da ta'addanci da sauran laifuffuka. (Fa'iza Mustapha)