in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Algeria ya nada sabon firaminista
2017-08-16 10:49:50 cri
Shugaban kasar Algeriya, Abdelaziz Bouteflika, a ranar Talata ya nada Ahmed Ouyahia a matsayin sabon firaministan kasar, inda ya maye gurbin Abdelmadjid Tebboune, kamfanin dillancin labarai na APS ne ya ba da rahoton.

Rahoton ya ambato cewa, an jayo shugaban kasar yana bayyana cewa, kudurin doka mai lamba 91 na kundin tsarin mulkin kasar ne ya sahalewa shugaban kasar ya kori Tebboune, bayan shafe kasa da watanni 3 a kan wannan mukami, kana ya maye gurbinsa da Ouyahia a matsayin sabon firaministan bayan tuntubar da ya yi wa mafi yawan mambobin majalisar dokokin kasar.

Sai dai majiyar ba ta bayyana cikakken bayani game da dalilan da suka haddasa wannan sauyi ba.

Ouyahia, wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar (RNS) mai mulkin kasar, kuma shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin kasar, ya sha rike mukamin firaministan a lokuta da dama, na baya bayan nan shi ne a shekarar 2012.

A nasa bangaren, Abdelmadjid Tebboune, bai yi karin haske dangane da tafiyar tasa ba. Ya ce abin da kawai zai iya fada shi ne har yanzu yana da cikakkiyar amincewa da shugaban kasar Bouteflika.

Sallamar da aka yi wa Tebboune, ta zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin ma'aikatan kasar suka fara sukan lamirinsa sakamakon alkawarin da ya yi na yaki da rashawa da rarrabe batun siyasar amfani da kudi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China