in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Aljeriya 5 sun mutu sanadiyyar hadarin jirgi mai saukar ungulu
2017-05-22 11:05:52 cri
A daren jiya Lahadi, wani jirgin sojin Algeriya mai saukar ungulu ya yi hadari a lardin Tipaza, dake yammacin babban birnin kasar Algeriyan, Algiers, hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan sojoji biyar dake cikin jirgin, kamar yadda kafafen yada labarun kasar suka tabbatar da hakan.

Jirgin sojin na Algerian ya yi hadarin ne a daidai wata gona dake Hamr el Ain a lokacin da yake gudanar da aikin shawagi a yankin. Jirgin dai ya samu matsala ne bayan da ya bugi turakun wutar lantarki, in ji rahoton da gidan talabijin na Ennahar TV ya watsa, shedun gani da ido ne suka tabbatar da lamarin.

Sai dai kawo yanzu babu wasu bayanai daga ma'aikatar tsaron kasar game da cikakken bayani dangane da hadarin.

A watan Maris na 2016, an samu makamancin hadarin jirgi mai saukar ungulu a arewacin Afrika inda ya hallaka sojoji 12 kana wasu biyu suka samu raunuka.

A shekaru 3 da suka gabata an samu hadduran jiragen saman sojoji a kasar ta Algerian hari mafi muni shi ne na jirgin saman samfurin C-130 a watan Fabrairun shekarar 2014, inda ya hallaka jami'an 77. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China