Wata majiya daga ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da cewa, dakarun sun kwace bindigogi kirar Kalashnikov guda biyar gami da albarusai da wasu abubuwan fashewa a hannun 'yan tawayen
Majiyar ta kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu dakarun kasar sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 8 tun lokacin da aka fara daukar matakan yaki da ayyukan ta'adanci a ranar 23 ga watan Yulin wannan shekara.
A kwanakin nan ne dai wasu 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar Al-Qaeda reshen yankin Maghreb (AQIM) suka kafa kungiyoyin Daesh inda suka boye a yankunan kungurumin dajin dake iyaka da kasashen Libya da Mali da suka yi fama da tashin hankali. (Ibrahim Yaya)