in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta fara kwashe 'yan kasar Nijar dake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba
2017-08-02 09:08:14 cri
A jiya Talata ne, mahukuntan kasar Aljeriya suka fara tusa keyar 'yan asalin kasar Jamhuriyar Nijar dake zaune a cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Abdelazia Benali Cherif ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne domin magance kwararar bakin haure cikin kasar ba bisa ka'ida ba, da kuma dakile kungiyoyin masu fataucin jama'a. Ya ce wannan na daga cikin matakan da kasar ke dauka don karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, wato Jamhuriyar Nijar da Mali, a wani mataki na magance kwararar bakin haure cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Benali ya ce aikin kwashe bakin hauren wanda ke gudana tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta kasar Aljeriya zai tabbatar da kare martaba da hakkin bil-Adama.

Gwamnatin Aljeriyar na shirin tusa keyar dubban 'yan gudun hijirar kasar Nijar zuwa gida kamar yadda mahukuntan Nijar din suka bukata tun a shekarar 2014, amma kuma wasu dubban 'yan gudun hijirar sun zabi zama a kasar ta Aljeriya, wasu da dama kuma na kokarin tsallakawa zuwa Turai. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China