Sellal ya bayyana gamsuwa da inganci da kuma fasahohin da aka yi amfani da su wajen gudanar da aikin. Bugu da kari ya yabawa ma'aikatan kamfanin na CSCEC wanda a halin yanzu ke gina tagwayen hanyar Trans-Sahara da ta taso daga mashigar arewa zuwa kudu, bisa kokarinsu na jure walhalhalu a yankuna masu duwatsu inda suke aiki ba dare ba rana.
Firaministan ya ce, nisan tagwayen hanyar da ta taso daga arewa zuwa kudu, wadda za ta hade kasashen dake arewacin Afirka zuwa kasar Najeriya, ya kai sama da kilomita 3,000 tana kuma da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasar ta Aljeriya da sauran kasashen Afirka da suka ratsa wannan hanya.
Ya kuma yi fatan kasar Aljeriya da bangaren kasar Sin za su karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta hanyar kammala wannan hanya mai muhimmanci cikin inganci.