in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya bukaci a ba tsarin siyasa muhimmanci yayin yi wa shirin wanzar da zaman lafiya garambawul
2017-09-21 10:05:05 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce dole ne a ba tsarin siyasa muhimmanci yayin da ake sake fasalin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Da yake jawabi ga taron kwamitin sulhu na MDD game da yi wa shirin wanzar da zaman lafiya garambawul, Sakatare Janar din ya gabatar da wasu shirye-shirye 4 na sake fasalin shirin.

Ya ce da farko, dole ne a lura da muhimmancin siyasa, ta yadda za a aiwatar da ayyukan wanzar da zaman lafiya bisa goyon bayan yunkurin diflomasiyya.

Ya ce na biyu shi ne, samar da kayayyakin aiki ga shirin, yana mai cewa, ingantattun kayayyakin aiki da na sufuri, da inganta horo da bayanan sirri za su ba da damar bunkasa ayyukan.

A cewarsa, na uku shi ne gudanar da ayyukan bisa tsare-tsaren MDD.

Har ila yau, Antonio Guterres ya ce, tun daga lokacin da ya kama aiki, ya aike da kwararan alamu dake bayyana kudurinsa na kawo karshen cin zarafin mata.

Ya kuma jaddada muhimmancin kara karfafa hadin gwiwa, yana mai cewa tsarin hadaka na MDD da Tarayyar Afrika kan inganta hadin kai ta fuskar zaman lafiya da tsaro da aka rattaba hannu cikin watan Afrilun bana, muhimmin mataki ne. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China