A jawabin sa Mr. Guterres ya ce ana ci gaba da kokari, na ganin an aiwatar da sauye sauye masu ma'ana, wadanda za su inganta, tare da kyautata tsarin aikin MDD, ta yadda za ta zamo mai alfanu, ta kuma gamsar da bukatun al'ummar duniya.
Ya ce yanzu haka MDD na fuskantar gyaran fuska, wanda ke bada zarafi na kara karfafa ayyukan ta. Sassan da ake yiwa gyaran dai a cewar sa, sun hada da na gudanarwa, da na saukaka tsarin aiwatar da shawarwari, da gudanar da ayyuka a bude, kuma bisa gaskiya da adalci.
A daya bangaren kuma, ya bayyana irin sauye sauye da ake fatan aiwatar nan ba da dadewa ba, a ayyukan wanzar da zaman lafiyar majalissar, da ayyukan raya kasashe, da ma matakan dakile nuna wariya, da nuna banbancin jinsi, da kuma yaki da cin zarafin bil'adama(Saminu Alhassan)