in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babbar muhawara a babban taron MDD karo na 72
2017-09-20 10:50:14 cri
A jiya Talata, an yi babbar muhawara a babban taron MDD karo na 72 a hedkwatar MDD dake birnin New York, inda wasu shugabannin kasashe da gwamnatoci kimanin 100 suka tattauna kan wasu kalubalolin dake gabansu da kuma matakan da za'a bi wajen tunkarar kalubalolin.

A wannan rana, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya gabatar da rahoton aiki na shekara-shekara, inda ya bayyana damuwarsa kan wasu kalubalolin da ake gamuwa da su a halin yanzu, da suka hada da batun nukiliya, sauyin yanani, masu tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci da dai sauransu.

Bugu da kari, shugaban babban taron MDD Miroslav Lechak ya gabatar da wani jawabi a yayin bikin bude babbar muhawarar, inda ya yi bayani kan babbar ka'idar MDD a yayin gudanar da ayyukanta, wato kiyaye zaman lafiya da kuma yin rigakafi kan aubkuwar rikice-rikice.

Haka zalika, ya sake jaddada alkawarin da babban taron MDD ya taba yi game da ba da taimako ga gamayyar kasa da kasa wajen aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030, da kuma aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata domin fuskantar matsalar sauyin yanayi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China