A yau Alhamis ne aka zabi jakadan kasar Georgia da ke kasar Spaniya Zurab Pololikashvili, a matsayin sabon babban sakataren hukumar harkokin yawon shakatawa ta duniya karkashin inuwar MDD wato UNWTO, yayin babban cikakken taron hukumar karo na 22 da ya gudana a birnin Chengdu na lardin Sichuan da ke kasar Sin.
Sabon babban sakataren hukumar ta UNWTO zai fara aikinsa ne daga shekarar 2018, kuma zai kammala wa'adinsa a shekarar 2021. (Tasallah Yuan)