in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ronaldo ya kaucewa furta wani abu bayan bayyanar sa a kotu
2017-08-02 17:47:27 cri
Tauraron kwallon kafar nan dan kasar Portugal wanda ke murza leda a Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya kaucewa furta wani batu game da tuhumar da ake sama ta kaucewa biyan haraji.

Ronaldo wanda ya bayyana gaban wata kotun kasar Sifaniya a ranar Litinin, ya bayyanawa kotun abun da ya sani game da zargin da ake masa, kana ya fice daga harabar kotun ba tare da zantawa da manema labarai ba.

Dan wasan mai shekaru 32 da haihuwa, ya sulale ba tare da sanin yan jaridar dake dakon fitowar sa daga kotun ba, sai dai daga bisani wakilin sa ya shaidawa masu farautar labaran cewa, Ronaldo ya yanke shawarar ba zai ce komai ba gare su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China