in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu ta doke Botswana a wasan neman gubin gasar cin kofin Afirka
2017-07-20 10:26:01 cri
Kungiyar kwallon kafa ta "Zebras of Botswana", ta sha kasha a hannun "Bafana Bafana" ta Afirka ta kudu da ci 2 da nema a gida, a wasan neman gurbin buga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2018.

Kungiyoyin biyu dai sun buga wasan ne a ranar Asabar 15 ga watan nan, a filin wasa na Francistown mai nisan kilomita 430 ,arewa maso gabas daga babban birnin kasar Gaborone.

Masu masaukin bakin dai sun yi duk mai yiwuwa domin ganin sun jefa kwallo a ragar kungiyar Afirka ta kudu amma hakan ya faskara, su kuwa a nasu bangare Bafana Bafana sun jefawa 'yan Botswana kwallaye biyun ne, daya kafin hutun rabin lokaci, kana dayar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China