Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Koci Mannetti ya bayyana farin cikin sa da wannan nasara, yana mai cewa ya ji dadi ganin yadda 'yan wasan sa ba su yi kasa a gwiwa ba, wajen jefa kwallon da ta ba su nasara a wasan da aka buga a gida.
Sai dai kuma ya ce, yanzu haka ba bu abun da ya rage masu illa maida hankali su ga sake samun nasara a wasa na biyu da za su buga a Harare fadar mulkin Zimbabwe a ranar 23 ga watan nan. Duk kungiyar da ta yi nasara a wasan na gaba, ita ce za ta kara da ko dai Comoros, ko kuma Lesotho, a zagayen karshe na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka da za a buga badi a kasar Kenya.
Koci Mannetti ya sake jaddada kwarin gwiwar sa, game da lashe wasan na ranar Lahadi mai zuwa, yana mai cewa za su doke Zimbabwe wadda ita ce ta lashe kofin COSAFA da aka kammala gasar sa ba da jimawa ba.(Saminu Alhassan)