Mr Lajcak wanda ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan bude zaman babban zauren majalisar karo na 72, ya ce yana farin cikin ganin yadda kasar Sin take ci gaba da taka wannan rawa da yadda take magana ba wai a matsayinta na kasa ba, amma a matsayinta na mai yayata manufofin MDD.
Ya kuma yi alkawarin cewa, zai yi aiki da dukkan kasashe mambobin majalisar, ta hanyar tuntubar juna don ganin an cimma nasarar manufofin da aka sanya a gaba. Kana ya ce, kofarsa a bude take ga kowa don karbar shawarwari masu ma'ana.(Ibrahim)