A jawabinsa shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajcak ya bayyana cewa, zai mayar da hankali a fannoni uku, wato yin aiki domin dan Adam, da martaba muradun bangarori daban daban, da kuma gudanar da ayyukan da kowa zai gani a zahiri. Kana ya jaddada cewa, ya kamata a yiwa dokokin MDD gyaran fuska, ta yadda MDDr za ta sa kaimi ga samar da yanayin da ya dace ga duniya.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, a yanzu haka duniya na fuskantar barazana da kalubale, a don haka yana fatan gwamnatocin kasashen duniya da hukumomin da abin ya shafa za su gaggauta cika alkawuran da suka dauka, ta yadda za a tinkarar irin wadannan kalubale da barazana tare. (Zainab)