Idan an dubi tarihi, za'a fahimci cewa, daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa ranar 7 ga watan Agusta, kana, daga ranar 13 zuwa 19 ga watan Satumba na shekara ta 2005, Sin da Koriya ta Arewa da Japan da Koriya ta Kudu da Rasha tare kuma da Amurka sun gudanar da shawarwari zagaye na hudu a birnin Beijing, inda suka fitar da wannan sanarwa da ake kira sanarwar ranar 19 ga watan Satumba.
A cikin wannan sanarwa, Koriya ta Arewa ta yi alkawarin cewa, za ta yi fatali da duk wani makamin nukiliya da ta mallaka gami da shirinta na kera makaman nukiliya, ita kuma Amurka ta ce, ba za kaiwa Koriya ta Arewa harin nukiliya ba.(Murtala Zhang)