Sanarwar ta bayyana cewa, Koriya ta Arewa tana inganta shirinta na raya makaman nukiliya ne domin takawa manufofin kasar Amurka na nuna kiyayya da barazanar makaman nukiliya, ta yadda za ta dauki matakan kare kanta.
Rahotanni na cewa, kasar Amurka ta tsara wani sabon daftarin sakawa Koriya ta Arewa takunkumi sakamakon gwajin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi a ranar 3 ga wata, kuma yau ne ake sa ran za a kada kuri'u kan daftarin a yayin zaman kwamitin sulhun MDD.
A farkon watan Agusta, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2371 game da batun nukiliya na zirin Koriya, kana ya yi Allah wadai da harba makamai masu linzami da za a iya harba su daga wata nahiya zuwa wata da kasar Koriya ta Arewa ta yi a ranakun 4 da kuma 28 ga watan Yuli, inda ya bukaci kasar Koriya ta Arewa da ta yi watsi da shirinta na makaman nukiliya da kuma makamai masu linzami, kana ya yanke shawarar saka mata karin takunkumi. (Zainab)