Wannan na kunshe ne cikin labarin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta wallafa a shafinta na internet a yau Asabar, game da batun sake harba makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa ta yi.
Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ta na mai da hankali kan kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya yanke kan batun harbar makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa ke yi, kuma ba za ta amincewa kasar ta sabawa kudurin kwamitin ba ta hanyar harbar makamai masu linzami da kasashen duniya ba su amince da shi ba.
Har ila yau, Geng Shuang ya cewa, kasar Sin ta kalubalanci Koriya ta Arewa, da daina daukar matakan tsananta halin zirin Koriya, ya na mai cewa, kasar Sin na fatan bangarori daban-daban da batun ya shafa za su yi taka-tsantsan don magance tsananta batun, da tabbatar da zaman lafiya a yankin. (Zainab)