in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan IS na yukurin komawa arewacin Libya
2017-09-04 10:14:00 cri
Kakakin rundunar sojin dake gabashin Libya Col Ahmad Mismari ya ce mayakan kungiyar IS na yunkurin komawa yankunan gabar teku dake arewacin kasar.

Col Ahmad Mismari ya wallafa a shafin Facebook cewa, mayakan IS na kokarin kaura daga lokaci zuwa lokaci cikin kananan tawagogi, daga yankunan Sahara na kasar Libya zuwa yankunan gabar teku.

Ya ce mayakan sun kuma sace wasu fararen hula daga yankin, amma jami'an sintiri na bibiyarsu.

Kakain ya yi bayanin cewa, kaurar na zuwa ne a lokacin dakarun tsaro na Benghazi da na gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD ke komawa yankin dake da nisan kilomita 20 daga gabashin birnin Sirte.

Rundunar sojin Libya karkashin manjo janar Khalifa Haftar ta shafe shekaru sama da 3 tana yaki da kungiyar IS a gabashin Libya, a wani matakin soji da Haftar ya yi wa lakabi da "Dignity" wato "Daraja".

A baya bayan nan ne manjo janar Haftar ya sanar da kwace iko da garin Benghazi tare da cin galaba a kan kungiyar 'yan ta'addar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China