in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka mutane 8 a yammacin kasar Libya
2017-08-28 09:43:49 cri
Rahotanni daga kasar Libya na cewa, mutane takwas ne suka gamu da ajalinsu kana wasu biyu kuma suka jikkata, sakamakon wani fada da ya barke jiya Lahadi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai dake zaune a kusa da binrin Trahona da mazauna garin Rqe'at mai nisan kilomita 40 kudu maso gabashin Tripoli, babban birnin kasar.

Wata majiya daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Libya, ta ce fadan ya barke ne tsakanin sassan biyu lokacin da masu dauke da makamai suka halaka wani mazaunin garin na Rqe'ak, lamarin da ya harzuka mazauna yankin, inda su ma suka mayar da martani ta hanyar wasu farma 'yan tawayen dake yankin, yayin da su ma 'yan tawayen suka yi kokarin kare kansu ta hanyar kaddamar da hare-hare da tankokin yaki da sauran makamai.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa, yawan wadanda suka jikata sanadiyar arangamar ka iya karuwa, sakamakon rashin motocin daukar marasa lafiya da za su shiga wurin da lamarin ya faru don kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.

Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko hukumar yankin Trahona game da wannan fada. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China