Taron ya samu halartar mambobin kungiyar da suka hada da India da Kazakhstan da Sin da Kyrgyzstan da Pakistan da Rasha da Tajikistan da Uzbekistan tare kuma da wakilan kwamitin zartarwa na kungiyar mai yaki da ta'addanci.
Yayin taron an amince da tsare-tsare da kudure-kudure da yarjejeniyoyi da nufin yaki da ta'addanci da tsatsauran ra'ayi.
Har ila yau yayin taron, an amince Kyrgyzstan ce za ta rike shugabancin kwamitin na yaki da ta'addanci daga watan Satumban bana zuwa Satumban 2018, sannan taron kwamitin na gaba zai gudana a watan Afrilun 2018 a kasar Uzbekistan. (Fa'iza Mustapha)