Mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Sin, Li Huilai ya bayyana a birnin Astana cewa, wannan wani muhimmin aikin diflomasiyya ne da kasar Sin ta gudanar da yankunan Turai da Asiya, lamarin dake da manufar kara raya kungiyar SCO, da neman samun bunkasa tare tsakanin membobin kungiyar.
Li Huilai ya ce, shugaba Xi Jinping ya tattauna da shugabannin kasashe daban-daban, inda suka yi musanyar ra'ayoyi dangane da yadda za su raya kungiyar SCO, da sauran wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da shiyya-shiyya.
Shugaba Xi da sauran shugabannin kasashen kungiyar, sun rattaba hannu kan Sanarwar Astana, wadda ta shelanta yaki da ayyukan ta'addanci, da cimma yarjejeniyar yaki da masu tsattsauran ra'ayi ta kungiyar SCO, tare kuma da amincewa da baiwa Indiya da Pakistan izinin zama membobi a kungiyar ta SCO.
Game da nasarorin da aka samu a yayin wannan taro, Mista Li Huilai ya ce, kasar Sin na ganin nasarorin sun kunshi abubuwa da dama da suka hada da niyyar baiwa Indiya da Pakistan izinin zama membobi a kungiyar SCO da ta karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin tsoffi da sabbin membobi da kuma ci gaba da tabbatar da zaman doka da oda a duk fadin duniya.
Sauran sun hada da nuna yabo ga babban dandalin tattaunawa kan shawarar ziri daya hanya daya tsakanin kasa da kasa wanda aka yi a watan Mayun bana a birnin Beijing da kuma kara habaka hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi tsaro, da tattalin arziki, da al'adu da sauransu.(Murtala Zhang)