in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan binciken kimiyya na Sin ya kammala binciken sinadarin sulphide a tekun India
2017-07-10 10:25:27 cri

Jirgin ruwan binciken kimiyya na kasar Sin mai lakabin "Xiangyanghong 10" ya kammala binciken sinadarin "polymetallic sulphide", a sassan tekun kudu maso yammacin India.

A ranar Lahadi ne dai jirgin na "Xiangyanghong ya dawo gida kasar Sin, bayan shafe sama da kwanaki 200 yana gudanar da wannan aiki, wanda kuma aka gudanar a fadin tekun da ya kai sakwaya mita 30,000, karkashin wata kwangila da kasar Sin ta sanya hannu da hukumar kasa da kasa mai lura da teku.

Da yake karin haske game da hakan, daya daga masanan da suka gudanar da aikin Li Huaiming, ya ce yayin wannan aiki, an yi amfani da jirgin nutso a teku na kasar Sin wato Qianlong 2, inda ya nutsa karkashin teku har karo 8, tare da kaiwa kololuwar zurfin mita 3,320 a karkashin ruwa. Kaza lika Qianlong 2 ya shafe sa'o'i 170, yayin aikin da ya kai tsawon kilomita 456 don gudanar da wannan aiki.

Li Huaiming, ya ce aiki ya samar da damar gwada ingancin jirgin nutso na Qianlong, jirgin da aka tabbatar na iya gudanar da ayyukan bincike na kimiyya, ko da kuwa a yanayi ne mai matukar tsanani.

Shi dai jirgin ruwan bincike na Xiangyanghong 10, shi ne irin sa na farko da kasar Sin ta kera da hadin gwiwar wani kamfani mai zaman kan sa, musamman domin gudanar da safiyon sassan teku.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China