in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar majalisar dokokin Afrika ta kudu ta sauya ranar da za a kada kuri'ar rashin tabbas kan Shugaba Zuma
2017-07-03 13:57:35 cri
Shugabar majalisar dokokin Afrika ta Kudu Baleke Mbete, ta sanya 8 ga watan Augusta a matsayin ranar da za a kada kuri'ar rashin tabbas kan Shugaban kasar Jacob Zuma.

Kakakin majalisar Moloto Mothapo, ya ce Baleke Mbete ta sauya ranar kada kuri'ar ne bayan ta tuntubi jami'iyyun siyasa da dake majalisar da kuma bangaren zartaswa.

A baya, shugabar majalisar ta sanya ranar 3 ga watan Augusta a matsayin ranar da za a kada kuri'ar.

Kakakin ya kara da cewa, a lokacin da aka yi tuntuba tare da sanya ranar da aka sauya, an manta cewa akwai taron da aka shirya gudanarwa a mako.

Har ila yau, Moloto Mothapo ya kara da cewa, Baleka Mbete ta kuma sanya ranar 14 ga watan nan na Yuli, a matsayin ranar karshe da jam'iyyun siyasa za su mika hanyar da suke ganin ta fi dacewa ta kada kuri'ar, wato cikin sirri ko kuma a bayyane.

Ya ce Shugabar Majalisar za ta yanke shawara kan hanyar da ta fi dacewa ta kada kuri'ar kafin sabuwar ranar da aka sanya wato 8 ga watan Augusta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China