Kwanan baya, mataimakin babban sakataren MDD kuma darektan hukumar tsara shiri kan muhalli na MDD Erik Solheim, ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, an yaba wa nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da kwararar hamada, kuma akwai sa ran ganin kasar ta more fasaharta ta yaki da Hamada tare da kasashen duniya, a yayin babban taron kasashen da suka amince su shiga yarjejeniyar kandagarkin kwararar hamada ta MDD karo na 13, da ma kuma a nan gaba.
Mista Solheim ya kara da cewa, a ganinsa, abu mafi muhimmanci shi ne a kasar Sin, hamada, ba wata matsala ba ce, maimakon hakan wata dama ce ta samar da ci gaba. Ya ce ana dasa itatuwa a hamada, wanda hakan ya samar da karin guraben aikin yi, da kuma damar yaki da talauci. (Tasallah Yuan)