in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar UNEP ta gabatar da rahoton tattalin arzikin yankin hamada na farko
2017-09-12 11:17:09 cri
Hukumar kare muhalli ta MDD UNEP ta gabatar da wani rahoto kan yanayin tattalin arziki a hamadar Kubuqi dake kasar Sin, a jiya Litinin, a wajen taron bangarorin da suka cimma yarjejeniyar tinkarar kwararar hamada ta MDD karo na 13, dake gudana a Ordos na kasar Sin.

Wannan rahoto, shi ne irinsa na farko da MDD ta taba gabatarwa kan tattalin arzikin wani wuri mai alaka da muhallin halittu.

Rahoton ya bayyana cewa, an dasa bishiyoyi a wasu yankuna dake cikin hamadar Kubuqi, wadanda fadinsu ya kai eka miliyan 9.69, kuma ta wannan hanya, an samar da kayayyakin da darajarsu ta zarce kudin RMB na Sin biliyan 500, gami da samun damar fitar da jama'a fiye da dubu 100 daga kangin talauci.

A nasa bangaren, babban darektan hukumar UNEP, kuma mataimakin babban Magatakardan MDD, Erik Solheim, ya ce dabarar da aka dauka wajen kula da hamadar Kubuqi ya bayyana yankin hamada a matsayin wata dama, maimakon matsala, sannan an yi kokarin hada aikin kawar da talauci da raya tattalin arziki.

A cewar jami'in, akwai bukatar koyon fasahohin da aka dauka a yankin hamadar Kubuqi na kasar Sin wajen tinkarar kwararowar hamada.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China