in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron yaki da kwararar hamada na MDD karo na 13
2017-09-13 10:03:32 cri

A jiya Talata ne, aka rufe babban taron manyan jami'an kasashen da suka daddale yarjejeniyar yaki da kwararar hamada ta MDD karo na 13 a birnin Ordos na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin.

Yayin taron, wakilai mahalartan taron sun tattauna game da tasirin da lalacewar filaye ke kawo mana, kana suka gabatar da shawarwari kan matakan da za a dauka domin cimma burin hana tsanantar kwararar hamada a fadin duniya nan da shekarar 2030.

A yayin bikin rufe taron, babbar sakatariya a ofishin kula da yarjejeniyar yaki da kwararar hamada ta MDD Monique Barbut ta mika wa shugaban hukumar kula da dazuka ta kasar Sin Zhang Jianlong lambar yabo ta "fitaccen mai yaki da kwararar hamada na duniya", inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako a wannan fannin, inda ta samar da fasahohin yaki da kwararar hamada ga sauran kasashe, ko shakka babu kasar Sin ta ba da babbar gudumawa a aikin hana lalacewar filaye a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China