Kwamishinan lafiya na jihar Haruna Mshelia, ya ce gwamnati ta shirya wani asibiti mai gadaje 30 domin inganta kula da mutane tare da takaita yaduwar cutar.
Kungiyar likitocin agaji ta duniya MSF ta ce cutar da ta barke a sansanin Muna Garage na birnin Maiduguri, ta tsananta ne sanadiyyar ambaliyar ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi makonni 3 da suka gabata ta haifar.
Shugabar Kungiyar a birnin Maiduguri Ann Cillers, ta ce jimilar mutane 200 ne aka kwantar a asibiti tun farkon barkewar cutar, inda aka sallami 100 daga cikinsu.
Ann Cillers ta kara da cewa, tun daga ranar Asabar da ta gabata sama da marasa lafiya 50 aka kwantar a wani asibiti da kungiyar ke kula da shi dake wani bangare na birnin. (Fa'iza Mustapha)