Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump ne suka tsai da kudurin shirya taron a yayin da suke halartar taron kolin kungiyar G20 a birnin Hamburg na kasar Jamus, Mr. Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya shelanta labarin nan.
Mr. Wang Yang, mataimakin firaministan kasar Sin da Mr. Steven Mnuchin, sakataren kudi na kasar Amurka da kuma Mr. Wilbur Ross, sakataren kasuwanci na kasar Amurka ne za su jagoranci wannan taron tattaunawa cikin hadin gwiwa, inda bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyin kan batutuwan da suke shafar tattalin arziki da cinikayya. (Sanusi Chen)