Firaministan kasar Li Keqiang, ya gana da sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, inda ya ce kasarsa za ta ci gaba da bada goyon baya ga hukumar.
Li Keqiang ya taya Tedros Adhanom murnar kama aiki a matsayin dan Afrika na farko da zai rike mukamin darakta janar na hukumar, inda ya ce hakan na da matukar muhimmanci wajen inganta kiwon lafiya a kasashe masu tasowa.
Ya ce kasar Sin na daukar rawar da WHO ke takawa na kula tare da inganta ciyar da harkokin kiwon lafiya gaba a duniya da muhimmanci matuka.
Li Keqiang da ya gana da Tedros Adhanom a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da bada goyon baya ga ayyukan hukumar, kuma a shirye take ta inganta hadin gwiwa da ita a fannonin da suka hada da shawarar "Ziri daya da hanya daya".
A nasa bangaren, Tedros Adhanom ya ce kasar Sin ta yi babban garambawul cikin sauri tare da inganta tsarinta na kiwon lafiya, wanda ya zama abun misali da koyi ga kasashe da dama.
Ya ce hukumar WHO na yabawa da kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi, na bunkasa harkokin kiwon lafiya a duniya tare da gudunmawar da take badawa, na magance bukatun kiwon lafiyar al'umma na gaggawa cikin har da annobar Ebola da murar H1N1, yana mai cewa, a shirye WHO take ta inganta hadin gwiwa da kasar. (Fa'iza Mustapha)