Mr Geng ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Abbas zai kawo ita ce ziyararsa ta hudu da ya kawo kasar ta Sin. Ana kuma sa ran yayin wannan ziyara zai tattauna da shugaba Xi da Firaminista Li Keqiang da kuma shugaban majalisar kafa dokoki ta kasar Sin Zhang Dejinag.
Bugu da kari, ana sa ran sassan biyu za su yi jusayar ra'ayoyi game da hadin gwiwar dake tsakaninsu, da batutuwan Palasdinawa da sauran batutuwan dake shafarsu.
Mr Geng ya ce kasar Sin tana goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa na neman hakkokinsu. Kuma kasar Sin a shirye take ta taka rawar da ta dace a kokarin da ake na yayata shirin zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Isra'ila. (Ibrahim Yaya)