Kasar Sin ta bayyayana kudurinta na kara daukar matakan bude kofa ga kasashen waje, tare da samar da yanayin harkokin kasuwanci da ya dace ga Sinawa gami da baki 'yan kasashen waje.
Firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin ganawarsa da tsohon firaministan kasar New Zealand John Key, ya ce tsarin tattalin arzikin kasar, hidimomi da kuma kayayyakin da masana'antun kasar suke samarwa su ne kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin.
Wasu alkaluma da mahukuntan kasar ta Sin suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya samu ci gaban da ba a taba zato ba na kaso 6.9 cikin 100 a watanni shida na farkon wannan shekara da muke ciki.
A don haka firaminista Li ya ce, kasarsa za ta kara bude kofofinta ga kasashen waje, kana tana maraba da karin kamfanonin kasashen waje da su zuba jari a cikin kasar. Ya kuma ba da tabbacin cewa, za a samar wa kamfanonin Sinawa da na baki 'yan kasashen waje yanayin kasuwanci mai cike da adalci. (Ibrahim)