in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tusa keyar 'yan Najeriya 135 daga Libya
2017-08-18 10:03:25 cri
A jiya ne mahukuntan kasar Libya suka tusa keyar 'yan Najeriya 135 zuwa gida karkashin shirin nan na mayar da bakin haure zuwa kasashensu na asali.

Wani jami'in hukumar shigi da fice ya bayyana cewa, bakin hauren mata da kananan yara, wadanda masu tsaron kan iyakokin ruwa na kasar ta Libya suka ceto a tekun Medatareniya, a kokarin da suke yi na tsallakawa kasashen Turai.

An dai gudanar da aikin tusa keyar bakin haure ne tare da hadin gwiwar kungiyar kula da kaurar jama'a da duniya domin mayar da bakin hauren zuwa kasashensu na asali. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China