in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan siyasar Libya na fatan kasar Sin za ta taka rawa ta fannin wanzar da zaman lafiya a Libya
2017-08-27 15:10:47 cri
A kwanakin baya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana matsayin da gwamnatin kasarsa ta dauka kan batun kasar Libya, dangane da haka ne kuma wasu 'yan siyasar Libyar ke fatan Sin za ta kara taka rawa wajen taimakawa Libya kawo karshen halin baraka da take ciki tare da farfado da tattalin arzikinta.

Wani babban jami'i na majalisar bada shawarwari kan harkokin kasa ta Libya, Ali al-Suweih ya ce, Libya na maraba da samun tallafi daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, musamman tallafin da kasar Sin za ta samar mata ta fannin raya tattalin arziki.

Ya kara da cewa, dangane da batun kasar Libya, gwamnatin kasar Sin na mutunta ikon mallakar yankin Libya, da goyon-bayan daidaita sabani ta hanyar gudanar da shawarwari tsakanin bangarori daban-daban.

Ali al-Suweih ya kuma nuna godiya ga matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka dangane da batun Libya.

Har wa yau, wani jami'i na daban a majalisar bada shawarwarin ta Libya, ya ce yanayin tsaron da kasar ke ciki zai yi babban tasiri ga yanayin tsaron da ake ciki a kasashen dake makwabtaka da ita, kuma ya zama dole kasa da kasa su mutunta, gami da kiyaye ikon mallakar yanki na Libya. Wannan jami'i ya ce, suna fatan gwamnatin kasar Sin za ta kara taka rawar gani wajen warware matsalar Libya yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China