Firaiministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci shiyyar arewa maso gabashin kasar da su aiwatar da shirin garambawul don samun ci gaba.
Li, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci cibiyar kasuwanci mai 'yanci ta lardin Liaoning, inda ya samu zantawa da ma'aikatan kamfanin game da yadda ayyukansu ke gudana.
Shiyyar arewa maso gabashin Sin, ta kasance muhimmin tushe na habaka ci gaban tattalin arziki kuma mai dubun arziki ce, kana za ta iya yin tasiri a matsayin cibiya ta gwaji don gudanar da cinikayya mai 'yanci domin zama wani muhimmin wajen da zai jagoranci aiwatar da shirin garambawul a wannan shiyyar, in ji mista Li.
Li ya kara da cewa, kamata ya yi kananan hukumomi sun bunkasa bangaren samar da kayayyaki, ta yadda za'a iya rage tsadar kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da hada hadar ciniki a matsayin wata hanya da za ta bunkasa kasuwanci a yankin da kuma janyo hankalin karin masu zuba jari.
A halin da ake ciki, ana samun karuwar ci gaban hanyoyin zamani a harkokin kasuwanci tare kuma da karuwar bukatun da abokan hulda ke da shi na irin kayayyaki da ayyukan hidima da suke bukata, wanda hakan na nufin wata babbar dama ce ga harkokin kasuwanci. Ya kamata masana'antu su inganta fasahohin da suke amfani da su, a cewar Li.(Ahmad Fagam)