Mr Li wanda ya bayyana hakan jiya Litinin yayin wani taron karawa juna sani, ya ce tsarin tattalin azriki na zamani yana da fa'ida matuka, duba da yadda ake kara cin gajiyar muhimman bayanai, da yadda ake biyan kudade ta wayoyin salula, da harkokin saye da sayarwa ta yanar gizo.
Don haka ya ce akwai bukatar tsoffin masana'antu su hanzarta bullo da managartan matakai ta yadda za su dace da zamani ba tare da gurbata muhalli ba.
Firaministan na Sin ya kuma yi fatan fasohohin sadarwa na zamani, za su taka rawa wajen bullo da sabbin sassan kasuwanci wadanda za su taimaka ga ci gaban tattalin arziki. Ya ce kamata ya yi mahukuntan kasar ta Sin su agazawa sabbin sassan sufuri da na'urorin zamani domin samar da hidimomi masu inganci ga jama'a. Kana a hannu guda, tsarin nan na "Internet Plus" zai taimaka wajen kawar da rufa-rufa a harkokin tafiyar da gwamnati.
Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2016 da ta gabata tsarin tattalin arziki ta yanar gizo ya samu karuwar kaso 18.9 cikin 100, daidai da RMB triliyan 22.6 kwatankwacin dala triliyan 3.4. (Ibrahim Yaya)