in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya Joao Lourenco murnar lashe zaben shugabancin kasar Angola
2017-09-07 18:52:51 cri

A yau Alhamis ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aike wa Joao Lourenco sakon taya murna, dangane da nasarar da ya samu ta lashe zaben shugabancin kasar Angola.

A cikin sakon shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Angola muhimmiyar abokiyar huldar kasar Sin ce a nahiyar Afirka. Ya ce yana dora muhimmanci kan ci gaban hadin gwiwar Sin da Angola, kana a shirye yake ya hada kai da sabon shugaban don kara samun nasarori wajen bunkasa hadin gwiwar sassan biyu bisa manyan tsare-tsare, ta yadda zai kasance mai fa'ida ga kasashen har ma da al'ummominsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China