in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya murnar bude bikin baje kolin kayayyakin Sin da kasashen Larabawa
2017-09-06 13:45:09 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar bude bikin baje kolin kayayyakin kasar Sin da kasashen Larabawa na shekarar 2017, wanda aka bude a yau Laraba, a birnin Yinchuan na lardin Ningxia dake kasar ta Sin.

A cikin sakon na sa, shugaba Xi ya jaddada cewa, a gun taron kolin da aka gudanar a watan Mayun bana game da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shirin "ziri daya da hanya daya", an bullo da wata manufa, ta kafa wata hanyar bunkasa zaman lafiya, da bude kofa, da habaka wadata, da kirkire-kirkire da wayewar kai a yankin da shirin ya shafa. Manufar da ta samu karbuwa matuka daga kasashen Larabawa.

Babban taken wannan bikin baje kolin dai shi ne "Azama domin samun wadata ta hanyar kirkire-kirkire", taken da ya dace da manufar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Ana kuma iya cewa, bikin ya samar da wani dandali na hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Kaza lika kasar Sin na fatan yin kokari tare da sauran kasashen duniya, wajen sa kaimi kan aiwatarwar da shirin "ziri daya da hanya daya", tare kuma da cimma burin shimfida zaman lafiya a fadin duniya baki daya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China