Mataimakin babban sifeton 'yan sandan kasar mai kula da shiyya ta takwas Salisu Fagge, wanda ya bayyana hakan, ya kuma baiwa daukacin 'yan Najeriya tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyinsu a yayin da kuma bayan shagulgulan babbar sallah.Haka kuma shiyyarsa ta kara yawan jami'an dake sintiri a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, duk da nufin kare rayukan matafiya.
Ya kuma baiwa matafiyan tabbcin cewa, an dauki tsauraran matakan da suka dace don ganin an magance duk wata barazanar tsaro.
Fagge ya ce, an kuma umarci kwamishinonin 'yan sandan jihohin Niger da Kaduna da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, da su samar da cikakken tsaro a yankunansu a yayin da kuma bayan sallar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta ayyana yau Jumma' 1 ga wata da kuma Litinin 4 ga watan Satumba, a matsayin ranakun hutu, don murnar bikin babbar Sallah ta bana.(Ibrahim)