in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi na jadadda kira ga jama'arta da suka kaura su koma gida
2017-04-18 09:35:19 cri
Gwamnatin kasar Burundi na jadadda kira ga jama'arta da suka tserewa rikicin kasar na 2015 da su koma gida.

Ministan harkokin cikin gida da al'amuran yau da kullum na kasar Pascal Barandagiye ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da rahoton watanni uku, na aikin wayar da kan al'ummar kasar da suka kaura.

Pascal Barandagiye, ya ce cikin watanni uku da suka gabata, an ci gaba da gangamin wayar da kan al'ummomin kasar dake neman mafaka a kasashe makwabta.

Ya ce suna karfafa musu gwiwar komawa gida domin su hadu su gina kasar su, ya na mai cewa, aikin na samun sakamako mai gamsarwa.

A cewarsa, tsoro ne ya sa wasu daga cikin mutanen suka kaura yayin da wasu kuma suka tsere saboda jita-jita da ake yadawa.

Ministan ya kara da cewa, an adana dukkan kadarorin wadanda suka tsere a kauyukansu.

Tun a shekarar 2015 ne kasar ta Burundi ta fuskanci rikici, lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya yanke shawarar tsawaita wa'adin mulkinsa zuwa karo na uku, abun da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar da yarjejeniyar Arusha ta shekarar 2000 da ta kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru 10 ana yi.

Rahatanni sun bayyana cewa, sama da mutane 500 ne suka rasa rayukansu lokacin rikicin.

Wasu alkaluma da hukumar kula da kaurar jama'a ta MDD ta fitar a ranar 10 ga wannan wata, sun bayyana cewa, tun bayan barkewar rikicin, sama da mutane 400,000 ne suka tsere zuwa makwabtan kasashe da suka hada da Tanzania da Rwanda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Uganda.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China