in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 19 sun mutu, yayin da wasu 5 suka jikkata sanadiyyar rikicin da ya barke a wani kauye a Nijeriya
2017-09-09 13:40:00 cri

Rundunar 'yan sandan Jihar Plateau dake yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya, ta ce mutane 19 sun mutu, yayin da wasu 5 suka jikkata sanadiyyar harin da ake zargin makiyaya dauke da makamai sun kai wani kauyen jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Peter Ogunyanwo, ya ce ana gudanar da bincike kan kisan na kauyen Ancha dake yankin Bassa.

Peter Ogunyanwo ya ce, sakamakon binciken farko-farko ya tabbatar da cewa wasu 'yan kabilar Fulani dauke da bindigogi ne suka kai harin.

Ya ce Fulani makiyayan na son daukar fansa ne kan kisan wani karamin yaro da aka yi a kauyen, wanda a ranar 3 ga watan Augusta aka ce ya bata.

Kwamishinan ya ce daga bisani an shaida musu cewa an samu gangar jikin yaron ba tare da kai ba.

Rahotanni na cewa, domin daukar fansar kisan yaron ne aka kaddamar da harin da sanyin safiyar jiya Jumma'a, inda makiyayan suka yi wa kauyen dirar mikiya, kwanaki 3 bayan samun gawar yaron.

Peter Ogunyanwo ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da yara 6. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China