in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin babbar sallah cikin kwanciyar hankali a jihar Bornon Nijeriya
2017-09-02 12:12:35 cri
Bikin babbar Sallah na bana, shi ne bikin da aka yi cikin yanayi mafi kwanciyar hankali a sama da shekaru 7 da suka gabata, a jihar mai fama da rikici a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Usman Durkwa, ya bayyana jiya a birnin Maiduguri cewa, an gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali a fadin jihar.

A kan haramta zirga-zirgar ababen hawa da gudanar da bukukuwan taron jama'a a duk lokacin da ake bukuwan addini, imma na Islama ko na Kirista, saboda fargabar abun da kaje ya zo a jihar da ayyukan kungiyar Boko Haram suka fi kamari.

Ana sanya mazauna yin bukukuwan addini a gida tare da sanya dokar takaita zirga-zirga saboda hare-hare da muggan ayyukan Boko Haram.

Usman Durkwa ya ce bikin na bana ya gudana cikin yanayi mafi kwanciyar hankali da lumana, ya na mai cewa, alamu ne da ke nuna cewa an fara samun zaman lafiya a jihar.

Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa, an umarci dukkan shugabannin riko na kananan hukumomin jihar 27 su gudanar da bukukuwan sallar tare da 'yan gudun hijira dake sansanoni.

Usman Durkwa ya kuma yabawa hukumomin tsaro bisa nasarorin da suka samu a yakin da suke da 'yan tada kayar baya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China