Shugaban hukumar Boniface Ortese wanda ya bayyana haka a Makurdi babban birnin jihar, ya ce ambaliyar da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar ya shafi iyalai sama da 2,769.
Da yake ganewa idonsa barnar da ambaliyar ta yi a Makurdi da kewayenta, Gwamnan jihar Samuel Ortom, ya ce ibtila'in ya yi sanadin raba dubban mutane da matsugunansu a yankunan kananan hukumomi 12 na jihar.
Ya ce Gwamnatin jihar ta dauki matakan kare sake aukuwar ambaliyar da ta auku a jihar a shekarar 2012 inda ta rutsa da iyalai sama da 4,000 tare da sanadin mutuwar mutane da dama.
A nasa bangaren, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA, ta kai dauki ga mutanen da ambaliyar ta shafa a jihar Benue nan take. (Fa'iza Mustapha)